Isa ga babban shafi
Najeriya

An gano man fetur a jihar Neja

Ma’aikatar lura da albarkatun karkashin kasa a Jihar Neja da ke Arewacin Najeriya, ta tabbatar da gano wasu rijiyoyi man fetur bakwai bayan binciken hadin gwiwa tsakanin Jami’ar jihar da kamfanin man kasar NNPC.

Kwararru sun tabbatar da gano rijiyoyin mai a kauyukan jihar Neja da ke tarayyar Najeriya.
Kwararru sun tabbatar da gano rijiyoyin mai a kauyukan jihar Neja da ke tarayyar Najeriya. REUTERS/Henry Romero
Talla

Kawo yanzu dai jami’an da ke aikin binciken sun mika kwafin rahoto biyu ga kamfanin na NNPC, yayinda daya ya rage musu Rahoto guda yanzu haka wanda da shi ne za a tabbatar da sakamakon.

Hajiya Ramatu Yar’Adua kwamishinar albarkatun karkashin kasa ta jihar Neja, ta ce nan gaba kadan jihar za ta bi sahun takwarorinta masu albarkatun man fetur.

Kwamishinar ta ce an gano rijiyoyin man ne a kauyukan Enagi, Kontagora, Gulu, Bakani, Kudu, Kutigi da kuma Makera.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.