Isa ga babban shafi
Najeriya

Kungiyar Kwadago ta shirya soma yajin aiki

Yan Nigeria sun sa idanu yau laraba domin ganin ko da gaske ne kiran da kungiyar kwadago ta yiwa ma'aikata da a fara yajin aiki zai yi tasiri ganin cewa kotun sasanta rikicin ma'aikata ta nemi a jingine yajin aikin sai nan gaba kadan.

Zanga zangar adawa da karin farashin man fetur a Najeriya
Zanga zangar adawa da karin farashin man fetur a Najeriya © Reuters/Akintunde Akinleye
Talla

 

Ministan shari’ar kasar  Abubakar Malami ne ya shigar da karar a gaban kotu, inda mai shari’a Babatunde Adejumo ya bukaci ma’aikata da su dakatar da shiga yajin aikin sai bayan gudanar da shari’ar a raanr 24 ga wannan wata.

To sai dai jama’a na ci gaba da kintsawa domin kada yajin aikin ya rutsa da harkokinsu.

Bayan ganawar  kungiyar da gwamnati dai an kasa cimma matsaya  duk da tsawon lokacin da suka shafe don ganin sun fahimci juna akan lamarin wanda ya haifar da cece-kuce a dukkanin fadin Najeriya.

Shugaban kungiyar kwadagon Ayuba Waba ya shaida wa manema labarai cewa,  karin farashin man daga Naira 86 zuwa 145 ba shi da wani alfanu, lura da cewa an dauki irin wannan matakin a bangaren wutar lantarki amma duk da haka ba a samu wadatuwar wutar ba.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.