Isa ga babban shafi
Transparency

An samu karuwar cin Hanci a Duniya

Wani rahoton kungiyar Transparency International yace an samu karuwar cin hanci a shekaru biyu da suka gabata, wanda ya karya farin jinin mahukunta ga al’ummar duniya musamman bangaren sharia’a da ‘Yan siyasa da kuma ‘Yan sanda.

Tambarin kungiyar Transparency Internetional
Tambarin kungiyar Transparency Internetional RFI/Persan
Talla

Binciken kungiyar yace kusan rabin mutanen duniya sun ce matsalar cin hanci ta yi kamari a shekaru biyu da suka gabata, kuma wani bangare na al’ummar duniya sun ce akwai toshiyar baki da suka ba Jami’an gwamnati.

Rahoton na Transparency ya gano cewa akwai gurguncewar amanar da ke tsakanin Mutane da Jami’an da ke kare su da suka hada da ‘Yan sanda da alkalai da kuma Jam’iyyun siyasa.

Mutanen da rahoton ya zanta da su a fadin duniya sun ce matakan da ake dauka wajen yaki da matsalar Cin hanci a duniya sun ragu tun a shekarar 2008 da duniya ta shiga matsalar tattalin arziki.

Rahoton binciken na bana shi ne mafi girma cikin rahotannin da aka fitar a shekarun baya game da matsalar cin Hanci. Rahoton ya ji ta bakin mutane 114,000 a kasashe 107 na duniya.

Cikin jerin sahun kasashe 10 da matsalar cin hanci da rashawa ta yi kamari, 8 daga cikinsu, kasashen Afrika ne, a cewar kakakin kungiyar Transparency.

A kasashe 36 na duniya, mutanen kasashen sun ce ‘Yan sanda ne a sahun gaba wajen karbar cin hanci, yayin da kuma a kasashe 20 suka ce bangaren Sharia’a ne. a kasashe 51 sun ce Jam’iyyun Siyasa ne a sahun gaba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.