Isa ga babban shafi
WHO-Lafiya

Kasashen duniya na wuce kimar amfani da maganin Bacteria

Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce, wasu kasashen duniya na afmani da maganin kashe kwayar cuta fiye da kima, in da ta ce, akwai bukatar daukan matakan gaggawa wajen rage amfani da shi ba bisa ka’ida ba.

Kwayar cutar Bacteria na bijire wa magani a yanzu sabanin a shekarun baya saboda yadda kwayar cutar ke samar da dabarun kare kanta daga tasirin maganin
Kwayar cutar Bacteria na bijire wa magani a yanzu sabanin a shekarun baya saboda yadda kwayar cutar ke samar da dabarun kare kanta daga tasirin maganin Flickr/sparktography
Talla

A yayin da Hukumar Lafiyar ta Majalisar Duniyar ta gargadi yawaitar shan maganin a wasu kasashe, a gefe guda kuma ta ce, wasu kasashen na karancin amfani da shi, abin da ke baranaza ga lafiyarsu.

Rahotan Hukumar Lafiyar ya yi nazari ne kan kasashen duniya 65, in da ta samu Netherlands da Birtaniya da Turkiya da Iran a matsayin kasashen da ke kan gaba wajen shan maganin fiye da adadin da aka gindaya a kowacce rana.

Kasar Mongolia ce, ta fi kowacce kasa a duniya kwankwadon maganin na kashe kwayar cutar Bacteria a cewar rahoton, yayin da Burundi ke kasan teburi a jerin kasashen da aka gudanar da binciken a kansu.

A bangare guda Hukumar Lafiya ta ce, kasashen Italiya da Spain da Japan na kan gaba wajen amfani da mataki na biyu na maganin kashe kwayar cutar duk da cewa akwai sharadin fara amfani da Penicllin a matakin farko kafin kai wa ga mataki na biyu na maganin, idan cutar ta ci tura.

Kasashen Amurka da China da India ba sa cikin jerin kasashen da aka gudanar da binciken a kansu.

A shekarun 1920 aka samar da maganin na kashe kwayar cutar kuma ya taka gagarumar rawa wajen yaki da cutuka irin Sanyin Hakarkari da Tarin Fuka da kuma Sankarau, sai dai a yanzu, kwayar cutar ta koyi dabarun bijire wa maganin, abin da ke nuna cewa, akwai babbar barazana a fannin kiwon lafiya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.