Isa ga babban shafi
Yugoslavia

Kotu ta wanke tsohon jami’in tsaron Milsevic daga zargin kisa

Wata kotun Majalisar Dinkin Duniya da ke Hague ta wanke wani tsohon jami’in tsaron marigayi jagoran Sabiyawan Bosnia Slobodan Milosevic da ake zargi da kafa rundunar ‘yan ina da kisa a lokacin yakin Yugoslavia.

Kotun Hague
Kotun Hague
Talla

Shidai wannan Jami'in tsaro ana zarginsa ne da laifukan kisa a lokacin kazamin rikicin Yugoslavia inda kotun ke nuna shakku game da ko sashen wadancan runduna za su iya aikata zarge-zargen da ake masu.

Hukumomi a Belgrade dai sunyi marhaban da wannan hukunci na kotun kasa-da-kasa, inda suke ganin wannan zai bude kafar sasantawa da zaman lafiya a yankin.

Alkalin kotun ya bayyana cewa babu kwararan hujjoji da zai sa ya amince da zargin da aka yi cewa an aikata wancan laifi.

Sakin wannan jami’in tsaro, Jovica Stanisic , 62 da wani da ake zarginsu tare, Franko Simatovic, 63 na daga cikin jerin shari'oi da aka yanke hukuncinsu, duk da cewa masu shigar da kara sun nemi a daure mutanen ne na tsawon rayuwa.

Su kansu wadanda ake zargin sunyi zugum kafin yanke hukuncin, amma daga baya yanke hukunci sunyi ta nuna farin cikinsu a fili.

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.