Isa ga babban shafi
Korea ta Arewa

Korea ta Arewa ta sake gwajin makamin Nukiliya karo na biyar

A yau Litinin Kasar Korea ta Arewa ta sake gwajin makamin Nukiliya karo na biyar a kan tekun Japan a irin jerin atisayen gwajin makamin na nukiliya da kasar ke yi.  Wannan shine kwana na uku da Korea harba makain a jere.  

Nukiliyan da kasar Korea ta gwada
Nukiliyan da kasar Korea ta gwada REUTERS/KCNA
Talla

Kasar Korea ta kudu a jiya dama ta ce ba ta fidda tsammanin Korea ta Arewa za ta sake yin gwajin makamai masu linzami, kamar yadda ta yi a karshen makon a kan tekun Japan, lamarin da korea ta kudun da ma Majalisar Dinkin Duniya suka yi Allah wadai da si.

Mai Magana da yawun ma’aikatar tsaron Korea ta Kudu, Kim Min-Seok ya ce dakarun su, suna sa ido kan take taken a yankin na Arewan.

Tun da kasar ta yi gwajin makaman Nukiliya a watan Fabrairu, Majalisar Dinkin Duniya ta kakaba mata takukunkumi, kusan kullum sai hukumomin na birnin Pyongyang sun yi barazanar huce haushi a kan hukumomin birnin Seoul da ma Amurka.

Kakakin babban hafsan sojojin kasar ta Korea ta Kudu, ya ce babu tabbacin ko wane irin nau’in nukuliya Korea ta Arewan ke harbawa.

“Muna nan dai muna sa ido.” Inji Kakakin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.