Isa ga babban shafi
Wasan Tennis

Serena Williams ta tsallaka zagayen daf da na karshe, Djokovic ya sha kasa a hanun Haas

‘Yar wasan Tennis ta daya a duniya, Serena Williams ta samu nasara shiga zagayen daf da na karshe a gasar ATP Miami Masters da ake bugawa, haka shi ma Andy Murray ya yi nasarar shiga zagayen kusa da na karshe a bangaren maza. 

Serena Williams 'yar kasar Amurka lokacin da take gaisuwa ban girma ga 'yan kallo bayan ta doke 'yar kasar Afrila ta kudu Chanelle Scheepers.
Serena Williams 'yar kasar Amurka lokacin da take gaisuwa ban girma ga 'yan kallo bayan ta doke 'yar kasar Afrila ta kudu Chanelle Scheepers.
Talla

Hakan ya biyon bayan kayi da Li Na, ‘Yar kasar China ta sha a hanun Williams a yayin da Andreas Seppi dan kasar Italiya ya fadi a hanun Murray.

Sai dai Novak Djokovic ya fice daga gasar bayan Tommy Haas dan kasar Jamus ya doke shi da ci 6-2, 6-4.
“Akwai ranar da za ka ji ba ka jin dadin a filin wasan, wannan itace irin wannan ranakun.” Inji Djokovic.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.