Isa ga babban shafi
Wasan Tennis

Serena Williams ta janye daga gasar Dubai Open

Shararriyar ‘Yar wasan Tennis ta kasar Amurka, Serena Williams ta janye daga karawa a gasar Dubai Open kwanaki uku bayan an bayyana ta a matsayin ‘yar wasa ta daya a duniya a fagen wasan Tennis a bangaren mata. Williams ta bayyana cewa tana fama ne da ciwon baya wanda shine daya daga cikin dalilan da ya sa ta janye daga gasar.  

'Yar wasan Tennis Serena Williams a filin wasan gasar Australian Open a Melbourne
'Yar wasan Tennis Serena Williams a filin wasan gasar Australian Open a Melbourne REUTERS/Toby Melville
Talla

A dai ranar lahadin da ta gabata ne Victoria Azarenka ‘yar kasar Belarus ta doke Williams a gasar Qatar Open wacce ita ma janye daga gasar ta Dubai saboda wani ciwo da ta ke fama da shi a kafarta.

Williams dai ta ce zata mai da hankali kan gasar Miami da za gudanar a wata mai zuwa.

An dai saka kudi Dalar Amurka, miliyan biyu ga duk wanda ya lashe gasar ta Dubai Open.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.