Isa ga babban shafi
Tennis

Li na da Azarenka, za su buga wasan karshe a Australian Open

Li na ta China ta tsallake zagayen karshe bayan ta doke Maria Sharapova, kuma za ta kara ne da Victoria Azarenka wace ta doke matashiyar ‘Yar wasan Amurka Sloane Stephens da ta fitar da Serena Williams. Wannan ne karo na biyu da Li na ta tsallake zuwa zagayen karshe a Australian Open, kuma ‘Yar wasan tana neman lashe kofin ne karo na farko bayan lashe kofin Rolland Garros a 2011.

Li na ta China tana gaisawa da Maria Sharapova ta Rasha a Australian Open
Li na ta China tana gaisawa da Maria Sharapova ta Rasha a Australian Open REUTERS/Tim Wimborne (AUSTRALIA - Tags: SPORT TENNIS)
Talla

Azarenka kuma tana neman kare kambunta a matsayi jarumar Tennis ta Duniya idan ta doke Li na a wasan karshe.

A bangaren maza, Roger Federer ya tasallake zagayen kusa da karshe bayan doke Jo-Wilfried Tsonga, kuma a gobe Juma’a ne Federer zai kara da Andy Murray na Birtaniya.

A yau Alhamis ne kuma Novak Djokovic zakaran Tennis na Duniya zai kara da da David Ferrer a zagayen kusa da karshe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.