Isa ga babban shafi
Wasan Tennis

Nadal ya musanta cewa ba zai buga Gasar Indiana Wells ba

An sami rahotanni masu karo da juna akan dan wasan Tennis Rafael Nadal inda a yanzu haka dan wasan ya fito ya musanta rahotan da ke nuna cewa ba zai samu damar buga gasar Masters Series a Indiana Wells da Miami ba a wata mai zuwa.

Rafael Nadal
Rafael Nadal REUTERS/Toby Melville
Talla

A da rahotanni sun nuna cewa Nadal ya janye daga gasar domin yana shirin fafatawa a gasar French Cup da za a yi a watan Mayu mai zuwa.

Sai dai Nadal ya ce shi burinshi shine ya kasance a gasar ta Indiana Wells, sai dai ya bayyana cewa idan har ya ji wasan bai kwanta mai a rai ba, dole ne ya janye.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.