Isa ga babban shafi
Birtaniya

Birtaniya ta musanta zargin cewa ta kai jiragen yakinta Najeriya

Birtaniya ta yi watsi da zargin cewar ta kai jiragen yakin ta Najeriya dan kokarin ceto Dan kasar, Brendan Vaughan da aka sace a Jama’are tare da wasu ‘Yan kasashen waje. Sakataren harkokin wajen kasar, William Haque, ya ce jiragen da suka je Najeriya sun je ne domin kai dakarun kasar zuwa Mali.  

Firaministan Birtaniya, David Cameron
Firaministan Birtaniya, David Cameron REUTERS/Pascal Lauener
Talla

Wannan na kuma zuwa ne a dai dai lokacin da Birtaniyan ta yi Allah wadai da kisan da ake tsammanin an yiwa mutanen da ake garkuwa da su.

“Wannan mataki ne da ba za’a iya yafewa ba, domin kisan kai ne cikin ruwan sanyi, wanda babu wani dalilin yin haka, kuma alhakin hakan na kan wadanda suka sace mutanen.” Inji Hague.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.