Isa ga babban shafi
Japan

Matar da ta fi kowa tsufa a duniya ta yi bikin cika shekaru 115

Matar da ake zaton cewar yanzu haka ta fi kowa tsufa a duniya, Misao Okawa, ta yi bikin cika shekaru 115 yau a kasar Japan. Andai haife ta ne a ranar 5 ga watan Maris na shekarar 1898, kana ta yi aure a shekarar 1919, inda ta haifi yara uku, wanda yanzu haka biyu na na nan da ransu masu shekaru 90 a duniya. 

Matar da ta fi kowa yawan shekaru a duniya, Misao Okawa 'Yar kasar Japan
Matar da ta fi kowa yawan shekaru a duniya, Misao Okawa 'Yar kasar Japan s1.ibtimes.com
Talla

A karshen watan da ya gabata ne Okawa ta karbi shaida daga hukumar Guiness World Records da ya tabbatar cewa ita ce tafi kowa ywan shekaru a duniya.

A yanzu haka kasar Japan wacce ta yi fice wajen mutane da suka fi dadewa a duniya ita ke da mace da na miji da suka fi tsufa a duniya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.