Isa ga babban shafi
Japan

Majalisar Japan ta amince da karin kasafin kudin kasar da Dalar Amurka biliyan 142

Majalisar kasar Japan ta amince da karin kudi Dalar Amurka Biliyan 142 cikin kasafin kudinta na bana, yayin da Firaministan kasar, Shinzo Abe ya ke kokarin farfado da tattalin arzikin kasar da ya shiga wani hali. Wannan kudi a cewar rahotanni za a yi amfani da su ne wajen bunkasa harkokin kasuwanci da kuma karin guraben aiki a kasar har ila yau da magance matsalar girgizan kasa da wasu yunkuna ke fama da shi. 

Firamistan kasar Japan, Shinzo Abe
Firamistan kasar Japan, Shinzo Abe 路透社
Talla

Tattalin arzikin kasar ta Japan ya ragu sosai a tsakanin watannin Oktoba da Disambar bara, wanda hakan ya tsunduma harkokin kasuwanci cikin halin kakani-kayi saboda rashin fitar da kayyakin kasar zuwa kasashen waje.

Abe dai ya yi alkwarin farfado da tattalin arzikin kasar, inda ya nemi babban bankin kasar da ya fitar da tsare tsare masu inganci.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.