Isa ga babban shafi

Hare-haren masu ikirarin jihadi ya kashe fararen hula 22 a Burkina Faso

Wasu da ake zargin masu ikirarin jihadi ne sun kashe fararen hula 22 a wasu hare-haren da suka kai arewaci da kuma yammacin Burkina Faso, kamar yadda wasu majiyoyin tsaro da kuma na mazauna yankin da abin ya shafa suka bayyana.

Wasu da ake zargin masu ikirarin jihadi ne sun kashe fararen hula 22 a arewaci da kuma yammacin Burkina Faso.
Wasu da ake zargin masu ikirarin jihadi ne sun kashe fararen hula 22 a arewaci da kuma yammacin Burkina Faso. © Issouf Sanogo, AFP
Talla

Wata majiyar tsaro ta ce, masu aikin sakai da ke taimakawa sojoji 16 ne aka kashe a ranar Juma’a a arewacin kasar da ke fama da rikici, duk da rahotanni sun ce maharan ma sunyi asaran dakarunsu.

Wani mazaunin garin ya ce wasu fararen hula biyu kuma sun mutu a harin da aka kai wani kauye da ke kusa da Boulsa, babban garin da ke lardin Namentenga, inda ya kara da cewa maharan sun kuma kona gidaje da babura da kuma kasuwar yankin.

Wata majiyar tsaron ta ce an kuma kashe jami’an sakai 4 a wani harin da aka kai garin Fo da ke yammacin kasar duk dai a ranar ta Juma’a.

Garin Fo dai na fuskantar hare-haren masu ikirarin jihadi a ‘yan makwannin nan, lamarin da ya sanya mazauna garin ficewa daga cikinsa.

Tun a shekarar 2015 ne dai Burkina Faso ta fara fama da matsalar hare-haren masu ikirarin jihadi da suka ketara daga makwabciyarta Mali.

Wasu alkaluma da wata kungiya mai zaman kanta ta fitar sun nuna cewar, sama da mutane dubu 10 da suka hada da sojoji da ‘yan sanda da kuma fararen hula ne suka mutu a kasar sanadiyar hare-haren masu ikirarin jihadi, ya yin da wasu akalla miliyan biyu aka rabasu da matsugun nan su.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.