Isa ga babban shafi

Harin ta'addanci ya kashe mutane 12 a Burkina Faso

Akalla Fararen hula 12 ne aka kashe yayin wani hari da wasu da ake zargin mayakan masu ikirarin jihadi ne suka kai a yammacin Burkina Faso.

Sojojin Burkina Faso
Sojojin Burkina Faso © AFP
Talla

Majiyoyin tsaro da na cikin gida sun shaidawa kamfanin dillancin labarai na AFP cewar, tun daren Juma'a, wasu mutane dauke da makamai suka kai hari kauyen Sara da ke karamar hukumar Bekuy, kusa da Bobo-Dioulasso, birni na biyu mafi girma a kasar.

Shaidu suka ce, an binne gawarwakin mutane tara jiya  Asabar, sai kuma wasu mutane biyu suka mutu daga bisani sakamakon raunukan da suka samu, abin da yakai adadin wadanda suka mutu zuwa goma sha daya.

Wani mazaunin garin ya ce ‘yan ta’addan sun shiga kauyen ne da misalin karfe 8:00 na dare agogon GMT.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.