Isa ga babban shafi

Ba za mu kulla yarjejeniya da masu dauke da makamai ba - Burkina Faso

Firaministan Burkina Faso ya yi watsi da tattaunawa da 'yan tada kayar bayan da ke iko da yankunan kasar kamar yadda fadar gwamnati ta bayar da rahoton cewa an kashe mutane kusan 40 a sabbin hare-hare.

Traore ya kuma kori sojojin Faransa da aka tura domin taimakawa wajen yakar masu tada kayar baya a kasashen yankin Sahel da dama.
Traore ya kuma kori sojojin Faransa da aka tura domin taimakawa wajen yakar masu tada kayar baya a kasashen yankin Sahel da dama. REUTERS - VINCENT BADO
Talla

Apollinaire Kelem de Tambela ya shaidawa majalisar dokokin kasar cewa, ba za mu taba yin zaman shawarwari ba, kama daga batun da ya shafi yankunan Burkina Faso, ko kuma ikon mallakarta, inda ya kara da cewa gwamnatin kasar na da niyyar rubanya adadin masu aikin sa-kai na kungiyar VDP zuwa 100,000.

Kalaman nasa sun zo ne jim kadan kafin hukumomin yankin su fitar da sanarwar cewa, an kai hari kan ayarin motocin dauke da makamai a ranar Asabar a kusa da Bourasso da ke kusa da kan iyakar kasar da Mali.

Harin ya yi sanadin mutuwar mutane kusan 20, wadanda akasarinsu dakarun na VDP ne.

Gwamnatin yankin dai ba ta bayar da adadin wadanda suka mutu ba, amma ta yi ikirarin cewa an raunata mahara 18 tare da kama su.

Wata majiyar tsaro ta tabbatar da harin da aka kai kan ayarin motocin, inda ta kara da cewa daukin gaggawa da jiragen sama da aka kai ne ya taimaka wajen kashe 'yan ta'adda kusan 30.

Majiyar ta kuma ce an kashe wasu mutane 20 a wannan yanki a ranar Lahadin da ta gabata, lokacin da wasu da ake zargin masu tayar da kayar baya ne suka kai hari a Ouakara, wani kauye mai tazarar kilomita 100 daga Bourasso.

A shekarar 2022 ne mulkin kasar Burkina Faso ya koma karkashin jagorancin Kyaftin Ibrahim Traore, wanda ya sha alwashin kwato kashi 40 cikin 100 na yankunan kasar da ke hannun masu dauke da makamai masu alaka da Al-Qaeda da kungiyar IS da suka kwace tun a shekarar 2015.

Traore ya kuma kori sojojin Faransa da aka tura domin taimakawa wajen yakar masu tada kayar baya a kasashen yankin Sahel da dama.

Bayan hare-haren da aka kai tun daga farkon wannan shekara, gwamnatin mulkin sojan kasar ta sanar a watan Afrilun da ya gabata cewa, za a gudanar da taron gama gari na sojojin kasar.

Tun daga shekarar 2015, tashe-tashen hankula sun yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da 10,000, a cewar kungiyoyi masu zaman kansu, tare da raba wasu mutane miliyan biyu da muhallansu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.