Isa ga babban shafi

Sojojin Burkina Faso sun kashe 'yan ta'adda 50

Sojojin Burkina Faso sun samu nasarar kashe ‘yan ta’adda 50 a yankin arewacin kasar, farmakin sojin da ke zuwa bayan hare-haren 'yan ta'addan na makwannin da ke ci gaba da haddasa asarar rayukan fararen hula.

Sojojin Burkina Faso
Sojojin Burkina Faso MICHELE CATTANI / AFP
Talla

Da farko dai maharan sun yi wa dakarun Burkina Fason kwanton bauna ne a kusa da garin Tibou da ke lardin Loroum a kusa da iyakar Mali, a yayin da sojojin suke yi wa wani ayarin jami’an agaji rakiya, akan hanyar kai tallafin abinci zuwa wasu yankuna.

Bayanai sun ce baya ga ‘yan ta’addan da aka kashe, wasu fararen hula biyu sun rasa rayukansu yayin arrangamar.

Wadanda suka shaida aukuwar lamarin, sun ce adadin maharan da suka kai wa sojojin na Burkina Fason farmaki ya kai kato 100.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.