Isa ga babban shafi

Ina fatan tabbatuwar mafarkina don lashewa PSG kofin zakarun Turai - Mbappe

Bayan bajintar da ya nuna a daren jiya da ta baiwa PSG damar doke Barcelona da kwallaye 4 da 1 karkashin gasar cin kofin zakarun Turai, yanzu hankali ya karkata kan ko Kylian Mbappe zai iya amfani da damar ta karshe wajen lashewa kungiyar tasa kofin zakarun Turai.

'Yan wasan PSG na murnar chasa Barcelona.
'Yan wasan PSG na murnar chasa Barcelona. REUTERS - Juan Medina
Talla

Duba da yadda Mbappe ke taka leda a kakarshi ta karshe sanye da rigar PSG, kuma bajintarshi ta zura kwallaye 2 a wasan da suka yi waje da Barcelona mai tarihin lashe kofin gasar har sau 5, ya sanya kwarin gwiwa ga magoya baya don fatan ganin dan wasan ya kafa tarihi.

Mbappe dan Faransa mai shekaru 25 na sahun ‘yan wasa mafiya hazaka bayan da ya lashe kofin duniya da kuma kofunan Ligue 1 har guda 5.

Sai dai har yanzu tauraron na Faransa ya gaza ciyowa kungiyar tasa kofin zakarun Turai duk da irin kudin da PSG da zuba wajen kawo tarin ‘yan wasa da mabanbantan masu horarwa.

Yanzu haka dai PSG za ta hadu da Borussia Dortmund ne a wasan gab da na karshe na cin kofin gasar ta zakarun Turai dai dai lokacin da dukkaninsu ke kishirwar kofin.

A zantawarsa da manema labarai bayan tashi daga wasan na jiya Mbappe ya ce har yanzu ya na fatan ganin mafarkinsa na lashewa PSG kofin zakarun Turai ya tabbata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.