Isa ga babban shafi

Dan Najeriya ya shiga jerin manyan 'yan wasan Tennis 20 na Duniya

Wani rahoto da hukumar shirya gasar Tennis ta Duniya ITTF ta fitar a jiya ya nuna cewa Quadri Aruna ya shiga jerin manyan ‘Yan wasan Tennis 20 na duniya.

Aruna Quadri dan Najeriya lamba 1 a fagen Tennis a Afrika.
Aruna Quadri dan Najeriya lamba 1 a fagen Tennis a Afrika. NAN
Talla

A cikin jadawalin da hukumar ta fitar, dan Najeriyar ya samu matsayi na 19.

A jadawali 2 na baya-bayan nan da hukumar ta fitar, Aruna na matsayi na 22 bayan da ya yi rashin nasara a gasar cin kofin Tennis ta duniya wadda ta gudana a kasar Koriya.

Yayin da zakaran gasar a Nahiyar Africa Dan Kasar Masar Omar Assar, shima ya samu matsawa gaba zuwa matsayi na 16 a Duniya.

Zankaran Tennis a Nahiyar Africa Dan kasar Masar Omar Assar
Zankaran Tennis a Nahiyar Africa Dan kasar Masar Omar Assar REUTERS - LUISA GONZALEZ

Kazalika Aruna, na ci gaba da mamayar gasar ITTF ta 2024 wadda aka fara daga ranar Litinin 15 ga watan Afrilu, inda ya lallasa Daniel Gonzalez da ci 11 da 6, 11 da 4, 11 da 6, da kuma 11 da 6.

A yau Laraba ne ake sa ran Aruna zai buga wasa da Dan kasar Portugal Marcos Freitas, a filin wasa na Galaxy Arena.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.