Isa ga babban shafi
Commonwealth

Singapore ta janye daga karbar bakuncin wasannin kasashen renon Ingila

Kasar Singapore ta bi sahun Malaysia wajen yanke shawarar janyewa daga karbar bakuncin wasannin kasashen renon Ingila na Commonwealth da za a yi a shekarar 2026, abin da ke kara jefa makomar gasar wasanni da dama cikin shakku.

Wasu daga cikin 'yan wasan Kamaru yayin bikin bude gasar wasannin Commonwealth a Golad Coast a ranar 4 ga Afrilu, 2018.
Wasu daga cikin 'yan wasan Kamaru yayin bikin bude gasar wasannin Commonwealth a Golad Coast a ranar 4 ga Afrilu, 2018. REUTERS/Jeremy Lee
Talla

Hukumar shirya wasannin Commonwealth (CGF) ta yi ta kokarin ganin ta samu mai masaukin baki bayan da Australia ta fice a bara saboda tsadar rayuwa.

Malaysia ta fito a matsayin mai yuwuwar maye gurbin kasar amma ta ki amincewa a watan da ya gabata saboda matsalar kudi, duk da tayin dala miliyan 126 daga hukumar shirya gasar.

Ficewar Australia ba zato ba tsammani, da kuma rashin samun wata hanyar da za a bi, ya haifar da shakku kan makomar wasannin da ke gudana duk bayan shekaru hudu tare da janyewar wasu kungiyoyin da za su fafata daga kasashen da Birtaniyya ta yi wa mulkin mallaka.

A shekarar 2022 ne birnin Birmingham na kasar Ingila ya karbi bakuncin gasar ta karshe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.