Isa ga babban shafi

Gasar Olympics: Faransa ta ware tikiti miliyan guda da za a rabawa 'yan asalin kasar

Daga watan Afrilu, kusan tikiti miliyan daya za a rabawa ‘yan asalin Faransa, kama daga ’yan wasa masu tasowa, nakasassu da sauran su a wani yunkuri na fadada damar shiga gasar.

Faransa dai ta ce ta samar da matakan tsaro domin a gudanar da gasar cikin kwanciyar hankali.
Faransa dai ta ce ta samar da matakan tsaro domin a gudanar da gasar cikin kwanciyar hankali. AP - Michel Euler
Talla

Hakan na zuwa ne bayan sukar da aka yi cewa tikitin da ake sayarwa jama'a ya yi tsada sosai.

Za a raba tikitin kyauta tsakanin unguwanni da biranen Faransa da ke karbar bakuncin wasannin Olympics, a cewar kwamitin shirya gasar.

Daga cikin tikiti kusan miliyan guda, hukumar shirya gasar ta ce, 100,000 masu shirya gasar ne suka ba da gudummawar sa, wasu kuma gwamnatin kasar da hukumomin kananan hukumomi suka saya domin rabawa jama’a.

A Seine-Saint-Denis, wani yanki mai yawan jama'a a arewacin birnin Paris wanda ke karbar bakuncin manyan wuraren wasanni hudu , kusan tikiti 180,000 ne aka ware domin rabawa kyauta, inda 150,000 aka warewa masu kallon wasannin motsa jiki sannan 28,000 ga masu sha’awar halartar bikin bude gasar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.