Isa ga babban shafi

Alkalancin wasanni ya samu gagarumar koma baya a Ingila- Kompany

Mai horar da kungiyar kwallon kafa ta Burnley Vincent Kompany ya koka da yadda matsalolin alkalan wasa ke ci gaba da ta’azzara karkashin gasar firimiyar Ingila.

Vincent Kompany manajan kungiyar kwallon kafa ta Burnley.
Vincent Kompany manajan kungiyar kwallon kafa ta Burnley. AFP
Talla

Kompany na wannan korafi ne bayan da alkalin wasa Darren ya bashi jan kati yayin haduwar Burnley da Chelsea a karshen mako da suka tashi wasa canjaras kwallo 2 da 2.

Tun farko manajan ya yi kakkausar suka ne kan hukuncin alkalin wasan da ya bayar da fenariti ga Chelsea hukuncin da ya kai ga korar mai tsaron baya na Burnley Lorenz Assignon.

Cikin kakar nan kadai ‘yan wasan Burnley 6 aka baiwa jan kati tare da kora daga filin wasa a na tsaka da karawa, a wasanni 30 da zuwa yanzu kungiyar ta doka karkashin Firimiyar Ingila.

Jim kadan bayan tashi daga wasan bayan kuma karbar jan katin, Kompany wanda tsohon dan wasan City ne, ya ce kimar alkalan wasa na ci gaba da zubewa a Ingila, kuma akwai bukatar daukar mataki don dawo da kimar.

A cewar Kompany sam baya shakkar aci tararsa ko kuma a hukunta shi, kuma tun a lokacin ya shaidawa Darren ido-da-ido cewa yanayin aikinsa ba ya tafiya dai dai.

Kompany dan Belgium mai shekaru 37 ya ce halin da alkalanci wasanni ke ciki a Ingila ba batu ne da ke bukatar boye-boye ba, batu ne da ya kamata kungiyoyi su yi tarayya akai don samar da gyara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.