Isa ga babban shafi

Salah ya sake kafa tarihi bayan bajintarsa a wasan Liverpool da Brighton

Mohamed Salah na Masar na shirin shiga gaban Alan Shearer da Thierry Henry game da tarihin da suka kafa a gasar Firimiyar ingila bayan kwallon da ya zura a karshen mako da ta bai wa kungiyarsa Liverpool nasara da kwallaye 2 da 1 kan Brighton yayin wasan da ya gudana a Anfield wato gidan Reds.

Mohamed Salah na Masar da ke taka leda da Liverpool.
Mohamed Salah na Masar da ke taka leda da Liverpool. REUTERS - MOLLY DARLINGTON
Talla

Bayan kwallon ta ranar Lahadi, kenan Salah ya zura kwallaye 16 a wannan kaka, wanda ke nufin a tsawon kaka 7 jere dan wasan ya kafa tarihin taimakawa wajen zura kwallaye fiye da 25 kowacce kaka, walau kwallon da ya zura da kansa ko kuma wadda ya taimaka aka zura.

Wannan zarra ta bai wa Salah damar shiga sahun Henry da Shearer wadanda su kadai ke da wannan tarihi karkashin gasar ta Firimiya bayan da suka shafe kakar wasa 7 a jere suna taimakawa kungiyoyinsu wajen zura kwallaye 25 kowacce kaka.

Masu sharhi na ganin tauraron na Masar wanda har zuwa yanzu bai taba ciyowa kasar shi wani kofi ba, ya iya shiga gaban Henry da Shearer ganin cewa ya na da sauran kakar wasa guda gabanin karkarewar kwantiraginsa da Liverpool.

A jumlace tun bayan zuwansa Liverpool, Salah ya zura kwallaye 153 tare da taimakawa a zura 68 a wasanni 241 da ya doka wanda ke nufin dan wasan na zura kwallo guda a duk minti 91.

Haka zalika yayin wasan na ranar Lahadi, Salah mai shekaru 31 ya kuma kafa wani tarihin kai da kai wajen yunkurin zura kwallo da ke gab da shiga raga har sau 12 a wasa guda mafi, yunkurin da ke matsayin mafi yawa da ya taba yi a tarihinsa na Tamaula.

Haka zalika wannan ne karon farko da wani dan wasan Liverpool ya taba yin makamancin yunkurin tun bayan faro nadar kundin wannan kalubale a 2003 wanda ya bashi damar yin kankankan da Zlatan dan wasan da shi ma ya taba kafa tarihin irin wannan bajinta a 2016.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.