Isa ga babban shafi

Maurizio Sarri ya aje aikin horas da kungiyar Lazio

Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Lazio Maurizio Sarri yayi murabus daga aikinsa, bayan da kungiyar ta yi rashin nasara a wasanni biyar daga cikin 6 na baya-bayan nan da tayi a dukkanin gasannin da take ciki.

Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Lazio Maurizio Sarri yayi murabus daga aikinsa.
Mai horas da kungiyar kwallon kafa ta Lazio Maurizio Sarri yayi murabus daga aikinsa. AFP
Talla

A ranar Litinin data gabata, Lazio ta sha kashi a gida a hannun Udinese da ci 2-1, kari akan fidda ta daga gasar zakarun Turai da Bayern Munich ta yi a makon daya gabata.

A shekarar 2021 ce Sarri mai shekaru 65 ya amshi ragamar kungiyar, inda a kakar da ta gabata ya jagoranceta wajen karewa a mataki na biyu a kasar Serie A, mataki mafi girma da kungiyar ta taba karewa tun bayan da ta lashe gasar a kakar wasa ta shekarar 1999-2000.

Tuni dai kungiyar da a yanzu ke mataki na 9 a teburin gasar Serie A ta maye gurbinsa da mataimakinsa Giovanni Martusciello, a matsayin mai horaswa na rikon kwarya.

A baya dai Sarri ya yi aiki da kungiyar kwallon kafa ta Chelsea, inda ya jagorancita wajen lashe gasar Europa sannan ya kaita wasan karshe na gasar Carabao.

Kafin nan ya yi aiki a matsayin mai horas da kungiyar Napoli, inda ya jagoranceta wajen karewa a matsayi na biyu har sau uku a gasar Serie A, kuma ya samu nasarar lashe gasar da kungiyar Juventus a shekarar 2019 zuwa 2020.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.