Isa ga babban shafi

Liverpool za ta doka wasan karshe na Carabao ba tare da 'yan wasa 9 ba

Dai dai lokacin da Liverpool ke shirin karawa da Chelsea a wasan karshe na cin kofin kalubale ko kuma Carabao a ranar 25 ga watan nan Jurgen Klopp na fama da matsalar rashin zaratan ‘yan wasansa 9 wadanda ke jinyar rauni.

Masu sharhi na ganin zai yiwa Liverpool matukar wahala ta yi amfani da irin tawagar da ta kara da Luton a tsakiyar da mako wajen tunkarar Chelsea a ranar Lahadi.
Masu sharhi na ganin zai yiwa Liverpool matukar wahala ta yi amfani da irin tawagar da ta kara da Luton a tsakiyar da mako wajen tunkarar Chelsea a ranar Lahadi. © AFP - OLI SCARFF
Talla

Cikin wadannan ‘yan wasa kuwa har da wadanda bisa al’ada Klopp ya saba amfani da su a dukkanin manyan wasanni wadanda suka kunshi mai tsaron raga lamba daya wato Alisson Becker da Mohamed Salah sai Trent Alexandre-Arnold da Darwin Nunez kana Dominik Szoboszlai.

Sai dai duk da wannan rashin ‘yan wasa Jurgen Klopp a wata zantawarsa da manema labarai ya ce ko kadan baya shakkar kowacce haduwa da kowacce kungiyaa kuma karkashin kowacce wasa, domin kuwa a cewarsa matukar ya na da ‘yan wasa 9 walau daga karamar tawaga ko babba wasa zai tafi yadda ya kamata.

Ana ganin dai rashin ‘yan wasan har guda 9 zai tilasta Klopp amfani da wani salo kwatankwacin Wanda ya yi amfani da shi a wasan Liverpool da Luton ta hanyar gina tawaga mai tattare da ‘yan wasa masu kananun shekaru wajen tunkarar Chelsea a karshen mako.

Ko a wasan na Larabar da ta gabata, anga yadda Klopp ya tattaro ‘yan wasa daga karamar tawagar Liverpool ciki har da Trey Nyoni mai shekaru 16 da aka hango a benci.

Masu sharhi dai na ganin zai yiwa Liverpool matukar wahala ta yi amfani da irin tawagar da ta kara da Luton a tsakiyar da mako wajen tunkarar Chelsea a ranar Lahadi lura da cewa Blue din ta fara farfadowa dai dai lokacin da Reds ke fama da rashin zakakuran ‘yan wasan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.