Isa ga babban shafi

Bayern Munich ta yi rashin nasara 3 a jere cikin kwanaki 9

Bayern Munich ta yi rashin nasara a wasanni 3 a jere a cikin kwanaki 9, bayan da ta sha kashi a hannun Bochum da ci 3 da 2 a Lahadi. 

Bayern Munich  yayin daya daga cikin wasanninta a gida.
Bayern Munich yayin daya daga cikin wasanninta a gida. REUTERS - ANGELIKA WARMUTH
Talla

Bayern ce ta fara cin kwallo ta hannun Jamal Musiala ,kafin a dakatar da wasan har sau biyu sakamakon zanga-zangar magoya baya. 

Bochum ta ci kwallaye biyun ta daga Takuma Asano da Keven Schlotterbeck. 

Kevin Stoger ya ci kwallo daga bugun-daga-kai-sai-mai tsaron raga bayan da dan wasan baya na Bayern Munich Dayot Upamecano ya yi rafka a da’ira ta 18, aka ba shi jan kati. 

Wasa ya yi zafi, kuma duk da kwallon da kyaftin din Ingila, Harry Kane ya ci, wadda ita ce kwallonsa ta 25 a Budes Liga, Bayern ta gaza farkewa ballantana ta yi nasara. 

Yanzu Bayer Leverkusen ta bai wa Bayern Munich, a karkashin mai horarwa, Thomas Tuchel tazarar maki 8 a teburin Bundes Liga. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.