Isa ga babban shafi

Bayern Munich ta maimaita irin lallasawar da ta yiwa PSG a 2020

Kingsley Coman ya maimaita abinda Bayern Munich ta yiwa PSG a wasan karshe na cin kofin gasar zakarun Turai a 2020 yayin haduwarsu ta jiya talata karkashin ita dai gasar rukunin kungiyoyi 16. 

Wasa na 3 kenan a jere PSG na shan kaye a wannan kaka.
Wasa na 3 kenan a jere PSG na shan kaye a wannan kaka. REUTERS - CHRISTIAN HARTMANN
Talla

Kwallo 1 tal mai cike da bajinta da Coman dan Faransa ya zura ce ta baiwa kungiyar ta sa nasara kwatankwacin dai wadda ya ci a wasan karshe tsakanin kungiyoyin biyu shekaru 3 da suka gabata. 

Kingsley wanda ya taka leda da PSG a baya, ya zura kwallon ne bayan dawowa daga hutun lokaci ba tare da PSG ta iya farkewa ba, ko da ya ke Christophe Galtier ya sanya Kyllian Mbappe a fili amma a kurataccen lokaci. 

Mintuna kalilan da sako Mbappe ne dan wasan ya yi kokarin ceto PSG don farkewa inda ya zura kwallo a raga amma kuma aka bayyanata a matsayin ta satar fage ko kuma offside. 

Rashin nasarar ta jiya na nuna yadda PSG ta doka wasanni 3 a jere ba tare da ta yi nasara ba, wanda ake alakantawa da jinyar Mbappe. 

Ana ganin dai abu ne mai wuya PSG ta iya juya nasarar ta Munich idan ta je filin wasa na Alianze Arena a watan Maris. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.