Babu tabbacin Mbappe ya taka leda a wasan PSG da Bayern Munich
Yau ake dawowa wasannin gasar cin kofin zakarun Turai zagayen ‘yan 16, wato kungiyoyin da suka iya nasarar tsallakewa daga matakin rukuni inda a yau din za a gwabza tsakanin kungiyar Tottenham wadda za ta yi tattaki zuwa gidan AC Milan yayin da PSG za ta karbi bakoncin Bayern Munich.
Wallafawa ranar:
Wasu bayanai sun ce dan wasan gaba na PSG Kylian Mbappe ya koma atiisaye a jiya litinin gabanin wasan da kungiyar ta sa za ta doka wanda ke bayar da fatar yiwuwar dan wasan iya iya taka leda a karawar ta yau.
Mai horar da ‘yan wasan kungiyar ta PSG Christophe Galtier yayin wata tattaunawarsa a jiya litinin, ya ce bashi da tabbas kan yiwuwar ko dan wasan zai iya taka leda.
A cewar Galtier Mbappe ya yi atisaye tare da ‘yan wasan PSG a jiya kuma alamu nan una da karfi a jikinsa amma dole su jira abinda likitoci za su ce gabanin bashi dama.
A farkon watan nan ne Mbappe ya samu rauni a cinya wanda liktoci suka bayar da shawarar ya yi jinyar makwanni 3 gabanin dawowa filin wasa.
Haduwarta ta yau dai za ta tunowa bangarorin biyu karawarsu ta wasan karshe a gasar ta cin kofin zakarun Turai ta 2020 wadda PSG ta sha kaye da kwallo 1 mai ban haushi a hannun Bayern Munich.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu