Isa ga babban shafi

Fitattun 'yan wasan Bayern Munich sun baiwa hammmata iska

'Yan wasan gaba na Bayern Munich Sadio Mane da Leroy Sane sun baiwa hammata iska jim kadan bayan kayen da suka sha da 3-0 a karawar da suka yi da Manchester City a gasar zakarun Turai ranar Talatar da ta gabata.

Sadio Mane
Sadio Mane AP - Jon Super
Talla

Kungiyar ta Bayern Munich dai ta ki cewa komai akan lamarin duk da neman tsokacinta da manema labarai suka yi a jiya Laraba.

Bayanai sun ce naushin da Mane ya kirbawa Sane sai da  yayi  sandin darewar lebensa.

‘Yan wasan sun fara takaddama ne tun lokacin da ake gaf da karkar wasan da City ta lallasa su da kwallaye 3-0 a ranar Talata inda faifan bidiyo ya nuna yadda suka fara jayayya a filin wasa, wadda daga bisani wasu majiyoyi suka ce an fara ta ne bayann da Sadio Mane ya zargi  Sane da cewa ya raina shi.

Rashin nasarar dai ita ce mafi girma da Bayern Munich ta fuskanta a gasar zakarun Turai tun shekarar 2017.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.