Isa ga babban shafi

Bayern Munich ta doke Barcelona da kwallaye 2 da nema a gasar zakarun Turai

Kungiyar kwallon kafa ta Bayern Munich ta doke Barcelona da kwallaye 2 da nema a wasan da suka kara a daren jiya Talata karkashin gasar cin kofin zakarun Turai.

Leroy Sané ne ya zura kwallo guda cikin kwallaye 2 da Munich ta zura a wasan na jiya.
Leroy Sané ne ya zura kwallo guda cikin kwallaye 2 da Munich ta zura a wasan na jiya. REUTERS - LUKAS BARTH
Talla

‘Yan wasan Bayern Lucas Hernandez da Leroy Sane ne suka ci kwallayen biyun bayan da aka shiga zango na biyu, na wasan da aka kara.

Karo na farko kenan da Robert Lewondowski ya zaiyarci filin wasa na Alianz Arena, tun bayan rabuwa da Bayern Munich da yayi, inda ya koma Barcelona.

Lewandowski, wanda magoya bayan masu masaukin baki suka tarbe shi da jinjina, ya barar da damarmakin jefa kwallo a ragar tsohuwar kungiyar ta sa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.