Isa ga babban shafi

Zakarun Turai: wasannin da za su fi daukar hankali a karawar farko ta gasar

Yau Talata ake shirin doka wasannin farko na matakin rukuni a gasar cin kofin Zakarun Turai ta kakar wasan bana, gasa mafi kayatarwa da kuma daukar hankali ba kadai a nahiyar ta Turai ba, har ma da sauran sassan Duniya.

Akwai yiwuwar dai wasu kungiyoyi su bayar da mamaki a gasar ta bana.
Akwai yiwuwar dai wasu kungiyoyi su bayar da mamaki a gasar ta bana. © REUTERS/Murad Sezer
Talla

Sauyin shekar da ‘yan wasa suka yi daga tsaffin kungiyoyinsu zuwa inda suka koma taka leda a yanzu ka iya yin tasiri wajen sauya hasashen kwararru kan sha’anin tamaula dangane da rawar da su ke ganin manya da kananan kungiyoyi za su taka a babbar gasar kwallon kafar Turan da duniya ke zurawa idanu.

A yau Talata dai kungiyoyi 16 ne za su kara da juna a wasanni 8 da za a fafata.

Daga cikin wasannin na farko da za su dauki hankali akwai karawar da za a yi tsakanin PSG da Juventus, sai Celtic da Real Madrid, da kuma wasa tsakanin Sevilla da Manchester City.

A kakar wasan da ta gabata dai Real Madrid ce ta yi bajintar lallasa manya kungiyoyin da suka hada da PSG, Chelsea, Manchester City, da kuma Liverpool, kafin lashe kofin gasar Zakarun Turan.

Jerin nasarorin da Madrid zakarar La Ligar ta yi a bara ne zai sa magoya baya sanya idanu don ganin kamun ludayin kungiyar a wasan farko da za ta kara da Celtic, la’akari da sabon zubin ‘yan wasan tsakiya da suka hada da Aurélien Tchouameni da kuma Camavinga, bayan rabuwa da Casemiro.

Wasa tsakanin Manchester City da Sevilla ma zai dauki hankali, la’akari da cewar shi ne haskawar farko da fitaccen dan wasan gaba Erling Haaland zai yi a Manchester City cikin gasar Zakarun Turai bayan rabuwa da tsohuwar kungiyarsa Borussia Dortmund.

Zuwa yanzu dai tuni Haaland ya ci wa Manchester City kwallaye 10 a cikin wasanni 6 da ya bugawa kungiyar, abinda ke tabbatar da dan wasan mai shekaru 22 a matsayin kan gaba a duniya wajen kwarewar sarrafa tamaula zuwa cikin ragar abokan hamayya.

Wasa na uku da wasu masu fashin baki ke ganin zai dauki a yau kuma shi ne wanda za a fafata tsakanin PSG da Juventus.

Da farko dai za a iya kiran dukkanin kungiyoyin da manya a gasar Zakarun Turai, musamman la’akari da irin matsayin da suka kai cikin gasar a shekarun baya.

Sai dai kila hankali ya karkata kan zakarun gasar League 1 na Faransa, wadda ke da tawagar da ta kunshi fitattun ‘yan wasan da suka hada da Kylian Mbappe, Neymar da kuam Lionel Messi, hadin ‘yan wasan da ya sha caccaka a gasar Zakarun Turan kakar wasan da ta gabata, saboda gaza kai kungiyar PSG zuwa ko da zagayen wasan kusa da na karshe, duk da makudan kudaden da shugaban kungiyar ta PSG Nasser Al Kheleifi yake kashewa domin cefanen ‘yan wasa cikin fiye da shekaru 7 da suka gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.