City da Madrid sun lashe wasanninsu a gasar zakarun Turai
A jiya Talata ne aka dawo gasar lashe kofin zakarun Turai, inda aka fara wasannin zageye na biyu na gasar.
Wallafawa ranar:
A wasannin da aka yi, Manchester City da ke kare kambun ta kara da FC Copenhagen, inda ta samu nasara da ci 3-1, lamarin da ke nuna cewar kungiyar ta ci gaba da kokarinta na kare kambun wannan gasa da ta lashe a kakar wasan bara.
Kevin de Bruyne ne ya fara jefa kwallo a raga, kafin daga bisani Magnus Mattsson ya farke kwallon, bayan da mai tsaron ragar City Ederson yayi kuskuren bada kwallo.
Sai dai kafin a tafi hutu rabin lokaci, Bernardo Silva ya sake jefa kwallo wacce ta bai wa City damar shiga gaba a wasan.
A dayan wasan kuwa, Real Madrid ta samu nasara a wasan da ta yi da RB Leipzig.
Dan wasan tsakiya na kungiyar Brahim Diaz ne ya ci wa kungiyar kwallo daya tilo, da ta share mata hanyar zuwa matakin daf da na kusa da na karshe a karo na 12 cikin kaka 14.
A ranar Laraba 6 ga watan Maris ne za a yi kara wa ta biyu tsakanin Manchester City Copenhagen, sai kuma Real Madrid da RB Leipzig.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu