Kamaru tasha da kyar a hannun Guinea bayan da suka tashi 1-1
Tawagar kasar Guinea a gasar lashe kofin Afrika da ke gudana a Ivory Coast, ta rike takwararta ta Kamaru 1 da 1 a wasan farko na rukunin C da suka fafata a yammacin Litinin din nan.
Wallafawa ranar:
Guinea wacce ke mataki na 80 a jadawalin da Hukumar Kwallon kafa ta dDuniya FIFA ta fiar ce dai ta fara jefa kwallo a ragar Kamaru ta hannun Mohamed Bayo, kafin Frank Magri ya farke mata.
Tawagar ta Kamaru ta yi yunkurin kara kwallo, sai dai ta fuskanci turjiya daga wajen mai tsaron ragar Guinea Ibrahim Kone.
Wannan kunnen dokin ya sake bai wa Senegal damar jagorantar rukunin, ganin yadda ita kadai ce ta samu maki da kuma kwallo 3.
A wasan gaba, Kamaru za ta kara ne da Senegal ita kuma Guinea ta barje gumi da Gambia.
Sakamakon wasan dai ya ci gaba da bada mamaki a gasar lashe kofin Afrika da ke gudana a Ivory Coast, ganin yadda kasashen da suka yi suna a fagen kwallon kafar nahiyar ke shan mamaki a hannun masu tasowa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu