Isa ga babban shafi

Abubuwan da ya kamata ku sani game da gasar AFCON da ke gudana a Ivory Coast

A ranar Asabar 12 ga watan nan na Janairun 2024 aka fara gasar ta cin kofin nahiyar Afirka da aka fi sani da AFCON, wadda aka hada gwiwa tsakanin hukumar kwallon kafa ta Afirka CAF da kamfanin hakar mai da sarrafa albarkatunsa na TotalEnergies. 

Masar ce kasa mafi tarihin lashe kofin gasar ta cin kofin Afrika.
Masar ce kasa mafi tarihin lashe kofin gasar ta cin kofin Afrika. © CAF
Talla

An dai bude wannan gasa da wasa tsakanin mai masaukin baki Ivory Coast da kuma Guinea-Bissau a rukunin farko na A wanda yanzu haka Abidjan ke jagoranci da maki 3 bayan doke abokiyar karawar tata da kwallaye 2 da nema. 

A ranar 11 ga watan Fabrairu mai zuwa ne za a karkare gasar, wadda yanzu haka Senegal ke rike da kambunta. 

Tarihin gasar AFCON

Gasar cin kofin Nahiyar Afirka ta farko ta gudana ne a kasar Sudan cikin shekarar 1957. Sai dai a wancan lokacin, kasashe uku ne kawai suka buga gasar, da suka hada da Sudan din mai masaukin baki, sai Masar, da kuma Habasha, ba tare da buga wasannin neman cancantar shiga gasar ba. 

A waccan lokacin dai, an gayyaci Afirka ta Kudu zuwa gasar AFCON din ta farko a shekarar ta 1957, sai dai daga baya aka soke gayyatar, saboda dokokin wariyar launin fata, da turawa masu lukin Apartheid suka yi a kasar. 

A karawar farko ta gasar cin kofin kasashen Afirkan ta farko, Masar ce ta doke Sudan mai masaukin baki da kwallaye 2-1 a ranar 10 ga watan Janairun 1957. 

Raafat Atia ne ya kafa tarihin zura kwallo ta farko a gasar AFCON a ragar Masar yayin wasan kusa da na karshe da suka doke Sudan mai masaukin baki. 

Masar ce ta lashe kofin gasar AFCON din ta farko baya doke Habasha da kwallaye 4-0 a wasan karshe. 

Masar ta sake lashe gasar AFCON ta biyu a shekarar 1959 yayin da ta zo ta biyu a shekarar 1962, inda ta sha kashi a hannun Habasha mai masaukin baki a wasan karshe. 

Ivory Coast da ke karbar bakuncin gasar cin kofin kasashen Afirka ta bana, na yin hakan ne a karo na biyu, domin ta fara karbar bakuncin gudanar gasar kwallon kafar ce a shekarar 1984. 

Lokacin da kasar ta Ivory Coast ta karbi bakuncin gasar AFCON a shekarar 1984, kasashe takwas ne suka halarci gasar, wadanda suka hada da Algeria, da Kamaru, da Masar, da Ghana, da Najeriya da Malawi da kuma Togo. 

Masar ta fi kowace kasa lashe kofunan gasar AFCON da adadin guda bakwai sai Kamaru mai biyar, da Ghana hudu, sai Najeriya da ta lashe kofin sau uku, yayin da Jamhuriyar Dimokaradiyar Congo da kuma Ivory Coast mai masaukin baki a bana suka lashe bibbiyu kowannensu. 

A bangaren buga wasannin karshe kuma, Masar da Ghana ne ke kan gaba, domin kowannensu ya kai matakin karshen gasar ta AFCON har guda 9, daga cikin adadin kuma Masar ta lashe bakwai, Ghana ta lashe hudu, sai Kamaru ta buga wasannin karshe bakwai, inda ta lashe biyar daga ciki. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.