Isa ga babban shafi
AFCON

Senegal ta fara kare kambunta a gasar lashe kofin nahiyar Afrika da kafar dama

Tawagar Senegal ta fara kare kambunta a gasar lashe kofin nahiyar Afrika da kafar dama, bayan da ta doke tawagar Gambia da ci 3 da nema.

'Yan wasan Senegal, yayin da suke murna bayan nasarar da suka samu akan takwarorinsu na Gambia.
'Yan wasan Senegal, yayin da suke murna bayan nasarar da suka samu akan takwarorinsu na Gambia. © AFP / ISSOUF SANOGO
Talla

Tawagar ta Teranga Lions da ke karkashin jagoarancin Aliou Cisse na daga cikin wadanda suke sahun gaba wajen lashe gasar.

Mintuna 4 da fara wasanne Pape Gueye ya fara jefa kwallo a a ragar Gambia da ta kai matakin dab dana kusa dana karshe a gasar da ta gabata. Kafin zuwa hutun rabin lokaci kuma, Ebou Adams dan wasan Gambia ya samu katin kora.

Bayan dawowa daga hutun rabin lokaci ne kuma, Lamine Camara mai shekaru 20 ya jefawa kasarsa kwallaye 2.

Lokacin da Lamine Camara dan wasan Senegal ya jefa kwallonsa ta biyu a ragar Gambia.
Lokacin da Lamine Camara dan wasan Senegal ya jefa kwallonsa ta biyu a ragar Gambia. AP - Sunday Alamba

Senegal za ta buga wasanta na gaba ne a Kamaru wacce take cikin jerin manyan kasashen da masana ke hasashen za su taka rawar gani a wannan gasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.