Isa ga babban shafi

Real Madrid ta ci gaba da jagorancin La Liga bayan doke Mallorca

Kungiyar kwallon ta Real Madrid ta kara yawan tazarar da ta ke da shi a matsayinta na jagorar teburin La ligar Spain bayan nasara kan Mallorca da kwallo 1 mai ban haushi a daren jiya Laraba.

'Yan wasan Real Madrid.
'Yan wasan Real Madrid. AFP - GLYN KIRK
Talla

An dai kai ruwa rana a wasan na jiya wanda ya gudana a Santiago Bernabeu lura da yadda kowanne bangare ya gaza zura kwallo har zuwa bayan dawowa daga hutun rabin lokaci.

Sai a minti na 78 ne Madrid ta iya samun kwallonta ta hannun Antonio Rudiger wanda ya ci kwallon da kai bayan samun bugu daga Luka Modric, nasarar da ta ceto kungiyar daga komawa ta biyu a teburin na La liga.

Wannan nasara ta jiya ta sanya Madrid samun tazarar maki 3 cur a saman teburi ita da Girona da ke biye da ita a matsayin ta 2 kuma bayan wasan na jiya ya nuna cewa tawagar ta Carlo Ancelotti zuwa yanzu ta doka wasann 18 ba tare da anyi nasara akanta ba.

Yanzu haka dai Real Madrid na matsayin kankankan ne da Girona inbanda banbancin yawan kwallaye wanda Madrid din ke da 29 ita kuma Girona 22, amma kowaccensu ta doka wasanni 19 ne inda ta ke da maki 48.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.