Isa ga babban shafi

PSG ta buga canjaras 1-1 da Lille a gasar Ligue 1 ta Faransa

An tashi  kunnen doki a wasa tsakanin Lille da  PSG  a gasar  Ligue 1 ta Faransa, inda a kusan karshen wasan ne Lille  ta farke kwallo daya da PSG ta  makala mata a raga.

Dan wasan gaba na PSG, kylian Mbappe.
Dan wasan gaba na PSG, kylian Mbappe. REUTERS - DYLAN MARTINEZ
Talla

Kylian Mbappe ne ya ci wa PSG kwallo daga bugun daga-kai-sai-mai-tsaron raga, abin da ya sa ake ganin kungiyar tasa na daf da bada tazarar maki bakwai a saman teburin gasar ta Ligue 1.

Amma dan wasan Lille Jonathan David ya ci wata kwallo da kai, wasa ya koma 1 da 1.

PSG na da maki 37, kuma tana kokarin lashe gasar Ligue 1 na 10 a cikin kaka 12, inda ta bai wa mai bi da ita, Nice tazarar maki 5, a yayin da Monaco ke da maki 30 a matsayi na 3.

Duk da wannan abin takaici da ya faru, tawagar ta Luiz Enrique ta ci gaba da kasancewa a matsayin da ta shigo makon da shi, wato matsayi na daya.

Monaco ta sha kashi a hannun Lyon da ci daya mai ban haushi a Juma’a, kana Le Havre ta lallasa Nice, wadda ke matsayi na biyu a gasar da ci 3 da 1 a ranar Asabar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.