PSG na duba yiwuwar bayar da Mbappe a matsayin aro
Batun makomar dangantakar da ke kara yin rauni tsakanin PSG da tauraronta Kylian Mbappe na cigaba da daukar hankali, ganin yadda lamarin yaki ci yaki cinyewa.
Wallafawa ranar:
A yayin da Mbappe ya dage cewar sai ya karasa yarjejeniyarsa da kungiyar a shekarar 2024 ba tare da ya kara wa’adinta ba, majiyoyi kwarara sun bayyana cewar PSG ta fara Nazari kan yiwuwar aikewa da tauraron dan wasan na ta zuwa daya daga cikin kungiyoyin gasar Firmiyar Ingila a matsayin aro.
Wannan yunkuri na PSG na zuwa ne a daidai lokacin da jaridun wasanni na duniya da dama suka ruwaito cewar, kungiyoyin Chelsea da Tottenham da ma wasu kari, sun gabatar da tayin neman sayen Mbappe ko dai da zunzurutun kudi ko kuma hade da mika wasu daga cikin ‘yan wasansu.
Babban abin damuwa ga kungiyar PSG a halin yanzu dai shi ne rashin tabbas kan ko dan wasan na ta zai yadda ya koma wata kungiya a matsayin aro domin karasa yarjejeniyar shekara guda da ta rage tsakaninsa da zakarun gasar League 1 na Faransa.
Idan har bukatar PSG ta tabbata, hakan na nufin nauyin cigaba da biyan Mbapppe albashin tsawon shekarar da ta rage ya sauka daga kanta, yayin da kuma dan wasan zai samu damar rabuwa da kungiyar a matsayin dan wasan da babu wata yarjejeniya a kansa.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu