Isa ga babban shafi

Messi ya kama hanyar leshe wata gagarumar kyauta

An zabi Lionel Messi cikin jerin sunayen wadanda za su iya zama gwarzon dan wasa 'sabon zuwa' na gasar kwallon kafar Amurka ta Major League Soccer, da wasanni shida kacal da ya dokawa Inter Miami.

Gwarzon dan wasan Argentina a kungiyarsa ta Inter Miami da ke wasa a Amurka.
Gwarzon dan wasan Argentina a kungiyarsa ta Inter Miami da ke wasa a Amurka. AP - Erik Verduzco
Talla

Dan wasan gaban na Argentina, mai shekara 36, ​​ya koma kungiyar ne a watan Yuli, inda ya zura kwallaye 11 a dukkan gasar, tare da taimaka wa kungiyar ta Frank Lampard lashe gasar cin kofin Leagues na farko a tarihinta.

Sauran wadanda aka zaba domin lashe kanbin gwarzon ‘sabon zuwa’ na gasar MLS na bana, sun hada da dan wasan gaba na Atalanta United Giorgos Giakoumakis, da dan wasan tsakiya na St Louis City Eduard Lowen.

Ballon d'Or

Messi na kan gaba cikin wadanda ake kyautata zaton zasu lashe kyautar Ballon d’Or a Litinin mai zuwa bayan ya taimakawa Argentina lashe gasar cin kofin duniya ta 2022 a Qatar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.