Isa ga babban shafi

Messi na ci gaba da yin zarra a gasar kwallon kafar Amurka

Lionel Messi na ci gaba da haskawa a gasar kwallon kafar Amurka ta MLS, inda yake taimaka wa kungiyarsa ta Inter Miami wajen samun nasarori jere da juna.

Lionel Messi yayin kokarin ci wa kungiyarsa ta Inter Miami kwallo ta hanyar bugun falan daya
Lionel Messi yayin kokarin ci wa kungiyarsa ta Inter Miami kwallo ta hanyar bugun falan daya AP - Lynne Sladky
Talla

A ranar Lahadin da ta gabata, kwallaye biyu Messi ya ci wa kungiyar ta sa a wasan da suka tashi 4-4 tsakaninsu da FC Dallas, daga bisani kuma kungiyar ta Inter Miami ta doke Dallas da kwallaye 5-3 a bugun daga kai sai mai tsaron raga, nasarar  da ta basu damar tsallaka wa zagayen kwata final na gasar ‘Leagues Cup’

Da farko dai FC Dallas ce ke kan gaba da kwallaye 4-2 yayin fafatawar ta Inter Miami, har kuma zuwa minti  na 80 a ranar Lahadi, amma Messi ya sauya alkaluman cikin kankanin lokaci ta hanyar jefa kwallaye biyu.

A  halin da ake ciki, Messi ya ci kwalllaye 7 cikin wasanni 4 da ya buga wa Inter Miami mallakin tsohon dan was an Real Madrid da Manchester United David Beckham, tun bayan kulla yarjejeniya da kungiyar a watann da ya gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.