Isa ga babban shafi

Na sha matukar wahala kafin na saba da salon wasan PSG-Messi

Kyaftin Argentina Lionel Messi, ya bayyana yadda ya fara taka leka a tsohuwar kungiyarsa ta PSG da abu mai matukar wahala, sannan ya ce abin takaici ne yadda a lokacin zamansa a kungiyar suka kasa lashe gasar zakarun Turai.

Tsohon dan wasan PSG Lionel Messi,
Tsohon dan wasan PSG Lionel Messi, AP - Aurelien Morissard
Talla

Ya ce ya je kungiyar ne sabida yana sonta, kuma yana da abokai a can, amma sai dai abin mamaki ne yadda ya kasa sajewa cikin 'yan wasan kungiyar da wuri.

A shekarar 2021 Messi mai shekaru 36 ya kulla yarjejeniya da kungiyar PSG, bayan kawo karshen zaman shekaru 17 da ya yi a Barcelona.

A kakar wasansa ta farko kwallo 11 ne kadai Messi ya ciwa PSG a wasanni 34 da ya buga mata, lamarin da ya sanya magoya bayan kungiyar sukai ta sukar sa.

Messi da ya lashewa kasarsa kofin duniya da aka yi a shekarar da ta gabata, ya ce farkon zuwansa kungiyar magoya bayan na karfafa masa gwiwa, amma daga bisa al’amura suka suka sauya, duk da cewa mafi yawan magoya bayan kungiyar na tare da shi.

Bayan karewar kwantaragin shekaru biyu da ya kulla da PSG, Messi ya koma kungiyar Inter Miami da ke Amurka don ci gaba da wasa a can.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.