Isa ga babban shafi

Korarren kocin Spain ya karbi ragamar horar da tawagar mata ta Morocco

Tsohon manajan Spain, Jorge Vilda wanda tabargazar Luis Rubiales ta yi awon gaba da aikinsa, ya samu aikin horar da tawagar kwallon kafar mata ta Morocco.

Jorge Vilda ya rasa aikinsa ne na horar da tawagar kwallon kafar Spain bayan kin tsoma baki a badakalar sumbatar 'yar wasa Hermoso.
Jorge Vilda ya rasa aikinsa ne na horar da tawagar kwallon kafar Spain bayan kin tsoma baki a badakalar sumbatar 'yar wasa Hermoso. AFP - FRANCK FIFE
Talla

Vilda wanda ya jagoranci Spain wajen lashe kofin duniya na Mata bayan doke Ingila da kwallo 1 da nema, ya rasa aikinsa ne biyo byan boren da aka rika yi game da yadda yaki yin ala wadai da abin da Rubiales ya aikata a wancan lokaci.

Vilda dai ya ki cewa komi kan yadda Rubiales ya sumbaci 'yar wasa Jenni Hermoso jim kadan bayan nasararsu ta lashe kofin duniya, lamarin da ya haddasa masa kakkausar suka tare da neman lallai ya ajje mukaminsa.

Vilda mai shekaru 42 ya maye gurbin Reynald Pedros wanda ya taimakawa tawagar matan ta Morocco wajen samun tikitin gasar cin kofin duniyar ta mata karon farko har suka kai ga matakin wasan gab da na kusa da karshe gabanin Faransa ta yi waje da su daga gasar.

Rahotanni sun bayyana cewa, hukumar kwallon kafar Morocco da kanta ta bukaci Vilda ya zo don karbar aikin horar da ‘yan wasan nata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.