Isa ga babban shafi

'Yan kungiyar Al Ittihad sun ki buga wasa saboda ajiye gunki a kofar fili

An dage wasan kwallon kafar da aka shirya bugawa ranar Litinin, tsakanin kungiyoyin Saudiya da Iran a gasar cin kofin zakarun nahiyar Asiya, sakamakon ajiye mutum-mutumin tsohon babban kwamanda a rundunar sojin kasar Iran Manjo Janar Qassem Soleimani a kofar filin da za a fafata wasan.

Gunkin babban kwamanda a rundunar sojin kasar Iran Qassem Soleimani a kofar shiga filin wasa na Naghsh-e-Jahan da ke birnin Isfahan a kasar Iran. 2 ga Oktoba, 2023.
Gunkin babban kwamanda a rundunar sojin kasar Iran Qassem Soleimani a kofar shiga filin wasa na Naghsh-e-Jahan da ke birnin Isfahan a kasar Iran. 2 ga Oktoba, 2023. © Morteza Salehi, Tasnim News Agency via AP
Talla

Har zuwa wannan lokacin dai ba a sanya lokacin da za a kara tsakanin kungiyar Al Ittihad ta Saudiya da Sepahan ta Iran ba, bayan da tawagar ‘yan wasan Saudiya ta ki shiga filin da ke birnin Isfahan, saboda mutum-mutumin na marigayi Solaimani da aka ajiye a kofar shiga cikinsa.

Manjo Janar Soleimani dai ya taka muhimmiyar rawa wajen jagorantar ayyukan sojin Iran a Gabas ta Tsakiya tsawon shekaru da dama, kafin Amurka ta halaka shi a wani hari da ta kai masa a watan Janairun shekarar 2020.

Wannan sabani ya zo ne wata guda bayan da Saudiya da Iran suka kulla yarjejeniyar maido da wasannin kwallon kafa na gida da waje a tsakanin kungiyoyinsu, bayan da aka shafe shekaru bakwai bangarorin biyu basa ziyartar juna, sai dai su fafata a wata kasar.

Kungiyar Cristiano Ronaldo ta Al Nassr ce ta fara buga wasa a Iran cikin gasar Zakarun ta nahiyar Asiya a ranar 19 ga  watan Satumban da ya gabata, wanda kuma shi ne karo na farko da wata kungiyar kwallon kafa daga Saudiya ta shiga Iran tun shekarar 2016.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.