Isa ga babban shafi

Man-U: Zai yi wuya a shawo kan rikicin da ke tsakanin Ten Hag da Sancho

Rahotanni na cewa, da kyar ne a iya gyara dangantakar da ke tsakanin Sancho da Ten Hag ba tare da wanda ya shirya karbar laifinsa ba, yayin da Jadon Sancho ya yi imanin cewa yana da gaskiya na bayyana rashin amincewarsa a kana yar tambayar da Erik ten Hag ya diga game da irin gudun mowar da yake bawa kungiyar, a cewar majiyoyin daga kulob din, inda dan wasan na Ingila ke ganin ana nuna masa wariya, la’akari da yadda ake bawa abokan aikinsa fifiko.

Jadon Sancho kenan tare da Ten Hag
Jadon Sancho kenan tare da Ten Hag © Sky Sports
Talla

Dan wasan na Manchester United ya yi imanin cewa idan har ya nemi afuwa a yanzu to kuwa ya yarda cewa kocin ya fishi gaskiya, kuma hakan yana nufin ya gayyaci duk wani mataki na batanci da za a dauka a kansa.

Dan wasan dai na atisaye ne shi kadai tun ranar 14 ga Satumba kuma yana cin abinci tare ne da kananan ‘yan wasa a bangaren horaswar su, abin da ya sanya damuwa a zukatan wasu daga cikin ‘yan wasan gaba, musamman bayan Ten Hag ya jaddada matsayar sa da ke cewa rashin nasarar da United ta samu da ci 3-0 a hannun Crystal Palace 3-0 ya rataya ne a wuyan Sancho.

Damuwa game da kiyaye lokaci na Sancho da halin gaba ɗaya ba sabon abu bane. Sancho da kansa ya yarda cewa yana da matsala wajen kiyaye lokaci lokacin da ya makara don horon Borussia Dortmund a 2019 kuma kulob din ya ci tarar shi shekara guda bayan ya dawo daga Ingila a makare.

Rahotanni sun kuma nuna cewa wannan tanadin lokacin ya kasance matsala ga Sancho lokacin musamman kan makomarsa kan yadda yake taka leda a Ingila. Tun shekarar 2021 Gareth Southgate bai kira shi ba.

United ta tsaya tsayin daka kan matakin Ten Hag na kai tsaye kan halin dan wasan, inda majiyoyin kulob din suka nanata cewa dan kasar Holland din yana da goyon bayan darektan kwallon kafa John Murtough da Shugaban kungiyar Richard Arnold.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.