Isa ga babban shafi

Bonucci zai maka Juventus a gaban Kotu bisa zargin rashin mutunta shi

Mai tsaron baya na Italiya Leonardo Bonucci ya sanar da shirin daukar matakin shari’a kan tsohon Club dinsa Juventus saboda zargin da ya yi cewa ba a mutunta shi yadda ya kamata ba.

Leonardo Bonucci na Juventus.
Leonardo Bonucci na Juventus. AFP/Archives
Talla

Bonucci wanda ya koma Union Berlin cikin watan Agusta a kyauta bayan takaddama tsakaninsa da mai horarwa Massimiliano Allegri da ya kai ga kauracewa atisaye a cikin tawagar Juventus, ya ce ko shakka babu ya na ji a ransa cewa an ci zarafinsa a yanayin da ya raba gari da kungiyar.

Bonucci mai shekaru 36, ya yi ikirarin cewa kotu za ta kwato masa hakki kan cutarwar da Juventus karkashin jagorancin Allegri ta yi masa.

A cewar dan wasan bayan shafe shekaru 12 ya na taka leda da Juventus tare da lashe kofunan Serie A 8, bai samu karramawar da ya kamaci dan wasa kamar shi ba.

Bonucci wanda ya taimakawa Italiya wajen lashe kofin Euro 2020, ya fice daga tawagar Allegri da ta doka wasannin tunkarar sabuwar kaka a Amurka haka zalika bai doka dukkanin wasannin sada zumuntar da Juventus ta yi ba saboda kauracewa atisaye, sai dai ya ce hakan na da nasaba da yadda ya gaza samun damar atisaye da tawagar kungiyar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.