Isa ga babban shafi

Brazil ta ci tarar Neymar dala miliyan 3 saboda haka tafki a gidansa

Mai shigar da kara na gwamnatin Brazil ya ci tarar gwarzon dan wasan kasar, Neymar kimanin dala miliyan 3 da dubu 300 sakamakon yadda ya gina wani tafki a cikin katafaren gidansa da ke wajen birnin Rio de Janeiro.

Neymar na Brazil
Neymar na Brazil REUTERS - ISSEI KATO
Talla

Neymar ya gina tafkin ne ba tare da neman izini daga hukumomin kasar da ke kula da bangaren muhalli ba, yayin da kuma gwamnati ta katange tafkin tare da hana ci gaba da aikinsa.

Masu kula da muhallin su ce, dan wasan ya karya dokar kiyaye muhallin wajen gina tafkin.

Akwai wasu kafafen yada labarai na Brazil da suka bada rahoton cewa, dan wasan ya ma shirya wani biki a cikin tafkin, sannan ya yi wanka a cikinsa.

Kazalika hukumomin na Brazil sun samu Neymar da laifin karkatar da ruwan wani kogi zuwa cikin gidansa ba tare da neman izini daga hukuma ba, yayin da suka ce ya kuma tone kasa da hallaka tsirrai duk ba bisa ka’ida ba.

Yanzu haka dan wasan na da kwanaki 20 ya daukaka kara don kalubalantar hukuncin tarar da aka yanke masa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.