Isa ga babban shafi

City da Milan sun kai wasan daf da na karshe a Gasar Zakarun Turai

Manchester City ta tsallake zuwa wasan kusa da na karshe a gasar cin kofin zakarun Turai, bayan da suka tashi kunnen doki 1-1 da Bayern Munich a wasan daf da na kusa da na karshe da suka fafata daren Laraba a Allianz Arena.

'Yan wasan Manchester City.
'Yan wasan Manchester City. © AFP - OLI SCARFF
Talla

Erling Haaland ne ya ci kwallon daya tilon da ya baiwa City nasarar hada kwallo 4 – 1 jumulla a wasannin na gida da waje.

Haaland ya barar da bugun finareti a mintuna na 37, kafin dan wasan na Norway ya huce haushinsa ya zura kwallo a mintuna na 57.

Da wannan nasara da kungiyar ta Ingila ta samu a wasan kusa da na karshe a Champions League karo na uku a jere za ta hadu da Real Madrid wanda kamar yadda suka yi a kakar wasanni da ta gabata a daidai wannan mataki, Madarar ce ta yi nasara a wancan lokaci, ko tarihi ya mamaita kansa?

Inter Milan

Itama Inter Milan takai zagayen daf da na karshe a gasar cin kofin zakarun Turai, bayan da suka tashi 3-3 da Benfica, wato 5 - 3 jimilla.

Kungiyar Simone Inzaghi za ta kara da abokiyar hamayyarta na cikin gida AC Milan a wasan na hudun karshe, sakamakon kokarin kwallayen Nicolo Barella, Lautaro Martinez da Joaquin Correa.

'Yan wasan AC Milan bayan jefa kwallo a ragar Napoli
'Yan wasan AC Milan bayan jefa kwallo a ragar Napoli REUTERS - DANIELE MASCOLO

Kungiyoyin biyu na Milan na kokarin zama kungiyar Serie A ta farko da ta lashe gasar manyan kungiyoyin Turai tun bayan da Inter ta dauki kofin a shekarar 2010.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.