Isa ga babban shafi

Qatar ta gabatar da tayin sayen Manchester United

An dada samun karin haske kan rige-rigen da ake yi tsakanin masu kumbar susa wajen neman sayen Manchester United, bayan da a karshen makon da ya gabata, wata tawaga a karkashin jagorancin Shiekh Jassim Bin Hamad al-Thani shugaban bankin Musulunci na kasar Qatar, ta sanar da mika tayin neman mallake babbar kungiyar dake gasar Firimiyar Ingila.

Magoya bayan Manchester United yayin bayyana adawarsu ga Iyalan Glazer da suka mallaki kungiyar.
Magoya bayan Manchester United yayin bayyana adawarsu ga Iyalan Glazer da suka mallaki kungiyar. © AFP / OLI SCARFF
Talla

Sanarwar dai ba ta yi Karin bayani akan adadin kudin da tawagar kasar Qatar din ta gabatar domin sayen kungiyar ta United ba, sai dai wasu rahotanni na cewa, yawan kudin zai iya kaiwa dala biliyan 6.

A shekarar 2005 iyalan Glazer dake Amurka suka karbi ragamar shugabancin Manchester United, bayan mallake ta da suka yi.

Yanzu haka dai wannan kungiya na dauke da bashin da yawansa ya kai dala miliyan 620.

Watanni uku Kenan tun bayan da Iyalan Glazer suka sanar da aniyarsu ta ko dai sayar da United ko kuma hannayen jarinta, abinda ya sanya attajirai daga kasashen Qatar da Saudiya fara gogayya wajen cimma burin mallake kungiyar.

A halin yanzu dai Manchester United na matsayi na uku a gasar Firimiyar bana, nasarrar da suka samu biyo bayan karbar aikin horas da ita da Erik ten Hag yayi, kafin fara kakar wasa ta bana.

A ranar 26 ga watan nan na Fabarairu United za ta fafata da Newcastle a wasan karshe na gasar kofin Carabao, yayin da suke sa ran fitar da Barccelona daga gasar Europa a haduwar da za su sake, wadda suka yi tashi 2-2 da ita a Spain.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.