Isa ga babban shafi

An sanya wa jarirai fiye da 700 sunan Pele kwanaki kalilan bayan mutuwarsa

Hukumar kididdigar kasar Peru ta bayyana cewar a yayin da duniya ke alhinin rasa Pele gwarzon dan kwallon kafa na karni, sunansa zai rayu a tsakanin yara fiye da 700 ‘yan kasar da aka haifa a karshen shekarar 2022.

Pele
Pele REUTERS - STRINGER
Talla

Jerin sunayen da jami’an kasar ta Peru suka fitar ya nuna cewar, bayan mutuwarsa gwarzon dan kwallon kafar, an radawa jarirai 738 da aka yi wa rajista a hukumance sunan ko dai Pele, ko King Pele, ko kuma Edson Arantes ko Edson Arantes do Nascimento, cikakken sunan zakaran kwallon kafa na duniya sau uku.

A ranar 29 ga watan Disamba Pele ya mutu yana da shekaru 82 a duniya,wanda kuma aka binne shi a jiya Talata.

Iyayen yara a kasar Peru dai sun saba radawa ‘ya’yansu sunayen fitattun mutane da suke kauna walau a cikin ‘yan wasa ko kuma shugabanni, inda wata kididdiga ta nuna cewar a yanzu haka, sunan Cristiano Ronaldo ne aka fi radawa yaran kasar, wadanda adadinsu ya kai dubu 31 da 538.

Messi kuwa na da takwarori jarirai 371 ne a baya bayan nan a kasar ta Peru, wadanda ko dai aka sanya musu suna Leo Messi, ko Messi kadai bayan da ya lashe gasar cin kofin duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.