Isa ga babban shafi

Real Madrid ta ce ta kammala nazari a kan Jude Bellingham

Real Madrid ta kammala nazarinta kan dan wasan tsakiya na Ingila da ke taka leda a Borussia Dortmund ta kasar, Jamus Jude Bellingham, bayan sanya idon da tayi akan sa a lokacin gasar lashe kofin duniya da aka kammala a kasar Qatar.

Jude Bellingham.
Jude Bellingham. REUTERS - MOLLY DARLINGTON
Talla

Shima dai shugaban kungiyar ta Borussia Dortmund ya ce a yanzu ya ba wa dan wasan dama don nazari game da makomar sa a karshen wannan kaka.

Ya ce suna saran cinikin dan wasan ta zamo wacce tafi daukar hankali a kakar wasa ta badi, domin suna sa ran farashin dan wasan ya haura Yuro miliyan 100, ganin rawar da ya taka a gasar cin kofin duniya da ta kara daukaka darajar sa.

Real Madrid dai na son dauko dan wasan a kaka mai zuwa, domin dai suna ganin dashi sun kammala shirya tsakiyar su, ganin dai sun kawo Eduardo Camavinga da Aurelien Tchouameni da kuma Endrick, don haka suke ganin kawo Jude Bellingham ne kawai ya rage musu.

Rahotanni dai na nuna cewa dan wasan na sane da sha’awar sayo shi da Madrid ta nuna, kuma ya san irin nasarorin da zai iya cimmawa idan ya koma kungiyar sabanin wasu kungiyoyi, don haka al’amura na hannun sa ko dai ya shiga cikin tarihi ko kuma ya rasa damar sa kamar yadda wasu ‘yan wasa suka yi.

Daga cikin kungiyoyin Ingila da suka nuna sha’awar kawo dan wasan akwai Liverpool da Manchester City.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.